Labarai
Trending

An Hallaka Mutum Uku A Yayin Ƴan Ƙungiyar Asiri Ke Faɗa A Jihar Ogun.

Daga Firdausi Ibrahim Bakondi

Akalla matasa uku ne aka kashe a wani sabon kisan da ‘yan kungiyar asiri suka yi a garin Sagamu na jihar Ogun, kamar yadda ‘yan sanda suka tabbatar a ranar Litinin din nan.

Daily Trust ta ruwaito cewa, kimanin mutane 20 ne aka kashe a cikin watan Satumba lokacin da ‘yan kungiyar Eiye da Aiye suka yi ta kashe juna.

Gwamnati ta kafa dokar hana fita domin dakile kashe-kashen.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa yan kungiyar sun koma kashe-kashen ne a ranar Juma’a inda suka harbe mutane biyu har lahira a unguwar Latawa da ke Sagamu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Omolola Odutola, ya tabbatar da cewa an samu mutuwar mutane uku a rikicin.

Ya kara da cewa, a sakamakon rikicin kungiyar asiri, an kama mutane uku wanda aka bayyana sunayensu da Oluwatosin Adeniro mai shekaru 25 da haihuwa sai Adebayo Oluwasun mai shekaru 35 da Segun Ademola dan shekara 38 da haihuwa.

Odutola ya ci gaba da cewa, kwamishinan ‘yan sandan jihar Alamutu Abiodun, ya kai ziyara Sagamu a duk karshen mako domin tabbatar da tsaron daukacin mutanen yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button