April 18, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Jami’ar Tarayya da ke Oye Ekiti ta naɗa sabon shugaba bayan tsige na kai kan zargin lalata

Kwamitin Gudanarwa na Jami’ar Tarayya da ke Oye Ekiti (FUOYE) ya nada Farfesa Olubunmi Shittu, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Jami’a mai kula da Harkokin Karatu, a matsayin mukaddashin shugaban jami’ar na tsawon watanni shidda.

Magatakardan jami’ar kuma sakataren kwamitin Mista Mufutau Ibrahim, shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa bayan taron gaggawa karo na bakwai da kwamitin ya gudanar ta yanar gizo.

A yayin taron shugaban jami’ar Farfesa Abayomi Fasina, ya nemi izinin tafiya hutun shekara-shekara da ya fara, kuma kwamitin ya amince da bukatar sa nan take.

A gefe guda an ruwaito cewa taron gaggawa na kwamitin ya kasance sakamakon rashin jin dadin da Ministan Ilimi Dakta Tunji Alausa ya bayyana, game da yadda Shugaban Kwamitin Gudanarwa na jami’ar Sanata Ndoma Egba, da sauran mambobi suka shugabanci batun zargin cin zarafin jima’i da aka yi wa Farfesa Abayomi Fasina.

Rahotanni sun ce Ministan ya fusata matuka da rahoton kwamitin bincike na kwamitin, wanda ake zargin ya yi watsi da zargin cin zarafin jima’i, sannan ya bada shawarar cewa babbar ma’aikaciyar jami’ar uwargida Folasade Adebayo, wadda ta zargi shugaban jami’ar da ta ba shi hakuri.

Wani jami’i da ya halarci taron wanda ya nemi a boye sunan sa, ya bayyana cewa Farfesa Fasina wanda wa’adin mulkin sa zai kare a watan Agusta, ya roki kwamitin da ya ba shi damar tafiya hutun shekara-shekara maimakon a dakatar da shi kai tsaye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *