December 11, 2024

Masu Garkuwa sun sace mutum 30 a jihar Katsina.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Wasu ƴanbindiga sun sace akalla mutum 30 da suka haɗa da maza da mata tare da dabbobi masu yawa a jihar Katsina.

BBC ta rawaito, lamari ya faru ne a garin Unguwar Daudu da ke cikin karamar hukumar Funtuwa da tsakar daren ranar Alhamis.

Mutane a yankin na cikin zulumi ganin cewa ba su iya zuwa gonaki ɗauko abubuwan da suka noma sanadiyar hare-hare da yin gurkuwa da jama’a da ‘yan bindigar ke yi domin neman kuɗin fansa.

Ƴan bindiga Sun Sanya Harajin Miliyan 10 Ga Wasu Ƙauyuka A Jihar Katsina.

Ƴansanda Sun Kama Wani Ɗan Kasar Aljeriya Da Bindigu A Zamfara.

Akwai Bindigogin AK47 Guda Dubu 60 A Sansanonin Ƴan Bindiga Ɗari 120 Cikin Jihohin Arewa Masu Yamma,-Rahoto.

Bayan abun da ya faru a garin na Unguwar Daudu, a garin Mai ruwa da ke maƙwabtaka da ƙauyen ƴan bindigar sun yi awon gaba da wasu mutane da su ka je daukar albarkatun gona a daji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *