Labarai
Trending

Ko Dai Kamen Ƴan Gala Da Hisbah Ke Yi Bai Yiwa Hukumar Ta Ce Fina-finai Ta Kano Daɗi Ba?

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Hukumar Ta Ce Fina-finai ta jihar Kano da ke Arewacin Najeriya, ta koka kan sumame da hukumar Hisbah ke kaiwa gidajen Gala a jihar, a wani mataki na kawo karshen ayyukan baɗala.

Tin da farko hukumar Hisbah ta kai sumame wasu gidajen rawa inda ta kama Ƴan Gala 15 a unguwar Fanshekara da ke birnin Kano.

Freedom Radio ta rawaito cikin wata sanarwa da Kakakin Hukumar ta ce fina-finan Malam Abdullahi Sani Sulaiman, ta fitar Lahadin ƙarshen mako ta ce “ƙorafe-ƙorafen da Hukumar ke samu daga masu gidajen Gala ya yi yawa kan yadda Hisbah ke kai sumame su kame masu Gala da kayan aikinsu.”

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa, doka ce ta kafa Gidajen Gala a ƙarƙashin kulawar Hukumar Tace Finafinai kuma ta ba su damar gudanar da ayyukansu ba tare da cin zarafi ko tsangwama ba.

Kuma doka ta sanya wa masu Gidajen Galar Sharuɗa waɗanda in sun karya hukuncin zai hau kansu, hakan na cikin manyan dalilan da ya sa aka kafa Hukumar Tace Finafinai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button