Wata Babbar Kotu ta jihar Kano a ranar Talata, ta ɗage yanke hukunci kan shari’ar da ake yi wa tsohon Gwamnan jihar Kano kuma Shugaban jam’iyyar APC na Ƙasa Dr. Abdullahi Ganduje da wasu mutum bakwai, dangane da zargin cin hanci da almundahana.
Gwamnatin jihar Kano ce ta shigar da ƙarar da ke da ƙididdigar tuhuma takwas a kan Ganduje, matar sa Hafsat Umar Ganduje, da wasu mutane shidda, kan laifukan da suka shafi cin hanci, almundahana da karkatar da kuɗaɗen gwamnati da suka kai biliyoyin naira.
Sauran wadanda ake tuhuma tare da Ganduje su ne Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Kamfanin Lamash Properties Limited, Safari Textiles Limited da kuma Lasage General Enterprises Limited.
Lokacin da aka kai shari’ar domin sauraron dukkan buƙatun da ke gaban kotu, lauyan Ganduje da matar sa Offiong Offiong (SAN), ya shigar da buƙatar ƙarin lokaci kuma ya roƙi kotu da ta amince da buƙatar.
Sai dai lauyan gwamnati Ayodeji Adedipe (SAN), ya shigar da amsa kan ƙarar wanda aka shigar tun ranar 22 ga Oktoba, 2024, inda ya maida martani ga dukan wadanda ake tuhuma.
Ya roƙi kotu da ta ƙi amincewa da ƙorafin masu ƙara saboda rashin cancanta.
Lauyan wanda ake tuhuma na ukku da na bakwai Adekunle Taiye-Falola, ya shigar da ƙarar samun shakku ranar 18 ga watan Oktoba 2024.
Lauyan wanda ake tuhuma na biyar Sunusi Musa (SAN), shima ya shigar da ƙarar shakku ranar 18 ga Oktoba 2024.