Daga Suleman Ibrahim Modibbo
A Najeriya shugaban Ɗariƙar Qadiriyya ta Afrika Sheikh Qaribullahi Nasiru Kabara, ya ɓukaci gwamnatin ƙasar, ƙarƙashin jagoranci shugaba Bola Ahamd Tinubu, da majalisun dokokin ƙasar, su dawo da tallafin man fetur da aka cire.
Sheikh Kabara, ya yi kiran ne, a lokacin da yake jawabi a wajen taron Maubikin Qadiriyya karo na 73 da aka yi a birnin Kano da ke Arewacin ƙasar, a ranar Asabar ta ƙarshen makon da ya gabata.
Tun bayan cire tallafin man fetur da shugaba Tinubu, ya yi a ranar farko da aka rantsar da shi a matsayin sabon shugaban ƙasar Najeriya, ƴan ƙasar ke ci gaba da fuskantar ƙarin kuɗin Man Fetur, wanda hakan ya jawo tsadar abinci da tsadar rayuwa, da shan wahala da masara ƙarfi ke yi, abinda ya sa da yawan ƴan ƙasar ke kokawa.
“Ina tunatar da magabatan mu cewa, sakamakon janye tallafin Man Fetur jama’a sun shiga cikin wani hali da gaske, abinci ya yi wahala, rayuwa ta yi tsada”, in ji Sheikh Qaribullah.
Gwamnatin Najeriya ta ce, ta janye tallafin ne saboda yadda wasu mutane ke yin babakere kan kuɗaɗen tallafin, da kuma yadda bayar da tallafin ke hana yin wasu ayyukan more rayuwa ga ƴan ƙasa, wanda gwamnatin ta ce, za ta karkatar da kuɗaɗen tallafin ga wasu ɓangarori na daban.
Saboda haka shugaban Ɗariƙar Qadiriyya ya ce, abinda ya dace gwamnati ta yi shine maganin illar ba wai ta cire abinda kowanne ɗan ƙasa ke jin daɗin sa ba.
“Muna roƙon Shugaban ƙasa tare da ƴan majalisar sa masu bashi shawara, da majalisar wakilai da ta dattijai, a zauna ayi wani tunani, wanda za a duba wannan damuwa da mutane suke ciki, ayi ƙoƙarin a maganci wancan abun, amma kuma a tabbatar da tallafin.”
ya kuma ƙara da cewa bai kamata illa da ke faruwa ta sa a kawar da alkairi ba, “illar za a kautar kuma a tabbatar da alkairin”, a cewar sa.
TikTok: Kotu Ta Ɗaure Wani Matashi a Gidan Yari Kan Ɓata Sunan Sheikh Qaribullahi Kabara.
Ya kuma yi fatan alkairi ga sabuwar gwamnatin tarayyar Najeriya, da ta jihar Kano, da kuma yi musu tini kan nauyin da Allah ya ɗora musu k’na kiyaye rayukan al’umma da dukiyoyin su, wanda ya ce, wajibi ne ko wani shugaba ya kiyaye mutuncin al’umma, domin kuwa Allah zai tambaye su.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Gwamnatin Kano ta tabbatar da za ta yi adalci da sauraron ƙorafe-ƙorafen al’ummar da aikin magance zai zayar ƙasa zai shafa a Bulbula tare da biyan diyya
-
Buba Galadima ya ƙaryata batun komawar Kwankwaso APC da Ganduje ya yi
-
NSCDC ta tura Jami’ai 415 a Zamfara don tabbatar da tsaro lokacin bukukuwan Easter
-
Ƴansandan Najeriya Najeriya sun cafke mutum biyu kan rikicin baya-bayan nan da ya afku a jihar Filato
-
Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da sabon kwamitin ƙidaya