Babbar jam’iyyar Adawa a Najeriya PDP ta sake dage taron Kwamitin Zartaswar ta na Kasa (NEC) zuwa ranar 15 ga watan Mayu.
A wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi, Sakataren Jam’iyyar na Kasa Sunday Udeh-Okoye, ya bayyana cewa an dage taron daga ranar 13 ga watan Maris domin kammala tarukkan shugabanni a matakin yanki, jiha, karamar hukuma, da mazabu, tare da yin karin tuntuba domin tabbatar da an gudanar da taron cikin kwanciyar hankali.
Taron ya fuskanci jinkiri sau da dama. An fara tsara shi ne a ranar 15 ga watan Ogasta 2024, daga baya aka mayar da shi zuwa 24 ga watan Oktoba, sannan aka daga zuwa 28 ga watan Nuwamba. Daga nan aka sake shirin gudanar da shi a watan Fabrairu 2025, kafin daga baya a sanya ranar 13 ga watan Maris, amma yanzu an sake sauya wa zuwa sha biyar ga watan Mayu.
Udeh-Okoye ya bayyana cewa an dauki matakin sake dage taron ne bayan dogon shawarwari da Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC), shugabannin jam’iyya, masu ruwa da tsaki, da manyan jiga-jigan jam’iyyar, ciki har da Kwamitin Amintattu (BoT), Gwamnonin PDP, da ‘yan majalisar dokoki na jam’iyyar.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
“Haɗakar da ake ƙirƙira da nufin ƙalubalantar Tinubu a 2027 za ta rushe nan ba da daɗewa ba”-Ganduje
-
Wike ya tabbatar da Fubara zai koma kujerar Gwamnan Rivers in ya nemi afuwa
-
Jam’iyyar SDP ta ce ba za ta shiga wata haɗaka ba a zaɓen 2027.
-
Ƙaramin Ministan Gidaje da Ci gaban Birane Yusuf Ata ya gargaɗi Kwankwaso kan batun jihar Rivers.
-
NNPP ta nesanta ta da Kwankwasiyya da su ƙungiyoyi ta na mai gargadin su dena bayyana kansu a matsayin cikakkun ƴaƴan jam’iyyar.