Notice: Constant DISALLOW_FILE_EDIT already defined in /home/martabaf/public_html/wp-config.php on line 98
"Yawan rashin nasarar Atiku a zaɓe na nuni da cewa Allah bai rubuta masa mulkar Najeriya ba"-Daniel Bwala - Martaba FM "Yawan rashin nasarar Atiku a zaɓe na nuni da cewa Allah bai rubuta masa mulkar Najeriya ba"-Daniel Bwala - Martaba FM

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Mai bai wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu shawara kan sadarwar manufofi, Daniel Bwala, ya shawarci tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da ya fice daga harkar neman shugabancin ƙasa, yana mai cewa hakan ba ƙaddararsa bace.

Atiku ya riga ya tsaya takarar shugaban ƙasa sau shida – ta hanyar fidda gwani ko a matsayin ɗan takara – kuma ana hasashen zai sake tsayawa takara a 2027, matakin da ke janyo muhawara tsakanin ‘yan siyasa da masu sharhi.

A wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Journalist Hangout na TVC ranar Litinin, Bwala ya ce yawan rashin nasarar Atiku a zaɓe na nuni da cewa Allah bai rubuta masa mulkar Najeriya ba.

“Ka Yarda Da Ƙaddara” – Bwala Ga Atiku

A cewarsa:

“Idan zan haɗu da shi a gaban-gidansa, zan ce masa: ‘Mai Girma Alhaji Atiku Abubakar, ka yarda da ƙaddara. Allah ne ke bayar da mulki ga wanda ya ga dama, kuma bisa ga alamu da abubuwan da ke faruwa, watakila ba Allah ne ya rubuta maka shugabancin Najeriya ba.’”

Ya kara da cewa Atiku zai iya taimaka wa ƙasa ta wasu hanyoyi, musamman ganin cewa sun yi abota da Tinubu na tsawon shekaru.

“Ku haɗu ku taimaka wajen gina Najeriya irin wacce ku biyun kuke mafarkin yi. Idan ka yi haka, zai zama a ƙarshen rayuwar siyasar ka, ka cika wasu daga cikin burinka ta hanyar abokinka.”

“Idan Ya Ci Gaba da Neman Takara, Zai Ƙare da Kaskanci”

Bwala ya gargaɗi cewa idan Atiku ya nace sai ya tsaya takara a 2027, zai iya gamawa da kunya, yana mai cewa:

“Yanzu haka daga cikin ‘yan siyasar da ke tare da shi, ya riga ya rasa kusan kashi 60 zuwa 70 na magoya bayansa.”

Hadin Kan Atiku da Obi Babbar Kuskure Ce

Bwala ya kuma yi tsokaci kan rade-radin cewa Atiku da Peter Obi na shirin haɗa kai a 2027, yana mai cewa hakan zai zama babban kuskure ga Obi.

“Peter Obi zai yi babbar asara idan ya yadda ya zama mataimakin Atiku. Wadanda ke bin Obi ba don jam’iyyar sa suke ba, don shi ne suke. Da zarar ya janye daga tsayawa takara kai tsaye, zai rasa yawancin magoya bayansa.”

Bwala ya ce har Obi kansa watakila ba zai ji daɗin irin wannan haɗin gwiwa ba.

Hadin Gwiwar Jam’iyyu a 2027 Zai Gagara – Bwala

A ƙarshe, Bwala ya ce duk wani yunƙurin kafa haɗin gwiwar jam’iyyu kafin zaɓen 2027 ya riga ya mutu tun kafin a haife shi saboda irin karɓuwa da tasirin da Tinubu ke da shi yanzu a faɗin ƙasar.

“Gwamnoni da ‘yan majalisa daga jam’iyyun adawa na shigowa. Mutane daga yankunan da suke da karfi a baya yanzu suna koma wa ƙarƙashin shugabancin Bola Tinubu. Kowa yana karɓar jagorancinsa.”

“Duk da cewa ba cikakken mutum ba ne, Bola Tinubu yana da zuciya da hangen nesa. A siyasar Najeriya ta yau, babu wanda ke da ƙarfin jawo mutane kamar sa.”

By Moddibo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *