Za A Samu Ambaliyar Ruwa A Kano Da Katsina da Zamfara Da Wasu Jihohin Arewacin Najeriya.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo
A Najeriya hukumar kula da yanayi ta ƙasar NiMet, ta yi gargaɗin samun ambaliya a wasu jihohin ƙasar sakamakon mamakon ruwan sama da za a samu a ƴan kwanakin nan.
Hukumar ta ce jihohin da suka haɗa da Kano, da Katsina, da Zamfara, da Jigawa da Kebbi da Kaduna, da kuma jihar Adamawa na cikin barazanar fuskantar ambaliyar ruwa, don haka ne ta yi kira ga mahukuntar jihohin su ɗauki matakan kare al’ummominsu.
BBC ta rawaito, Alhaji Bashir Idris Garga, darakta a hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriyar NEMA ya ce wannan ruwan saman da za ayi na kwana uku ba ƙaƙautawa zai sanya magudanar ruwa da ba a cika damuwa da yashe su ba, su cike wanda daga bisani ruwan zai malala har ya je yayi ɓarna.
“Saboda haka ya kamata a ɗauki mataki ƙwarai da gaske ya zama cewa ambaliyar bai yi ɓarna fiye da yadda ake zato ba,” in ji daraktan.