October 14, 2024

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Zancen Man Fetur Ya Sauka Zai Yi Wahala, -Ɗangote.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo da Fatima Suleman Suleiman Shu’aibu

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote kuma mamallakin matatar Man Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa babu yuwuwar samun saukin farashin mai a najeriya a yanzu duk kuwa da cewa matatar man sa zata fara siyar da Mai nan ba da jimawa ba

Dangote ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke zantawa da BBC Hausa, “zancen ya sauka ɗin zai yi wahala a haka, saboda in ka riga ka duba, a yau Fetur, kasan da can kamar a Saudi Arabia da ke su sun fi kowa mai ɗin kamar kusan kyauta ake ba da wa, amma in ka je yanzu za ka ga cewar Riyar biyu ne da ɗigo talatin da biyar zuwa talatin da 8, to in kai wannan ma kansa ka yi shi a kan Naira dubu ɗaya da ɗari shida Dala, ya fi naira dubu,” in shi.

Dangote ya bayyana hakan ne a matsayin bayar da amsa ga tambayar da aka yi mana, kan saukar farashin Mai.

Wannan dai na zuwa ne ne biyo bayan kara farashin mai a Najeriya a Talatar da ta gabata wanda ya jawo ce-ce ku-ce a tsakanin al’ummmar ƙasar.

Gwamnatin Najeriya Ta Bai Wa Ƴan Kasuwa Wa’adin Tata Ɗaya Su Rage Farashi.

SSANU Ta Sake Yin Kira Ga Gwamnatin Najeriya Kan Biyan Albashin Watanni 4 Da Aka Hana Su.

Gwamnatin Neja Ta Janye Dakatar Da Haƙar Ma’adinai A Jihar.

A cewar Dangote a yanzu ana cigaba da kulla yarjejeniyar kasuwanci tsakanin sa da kamfanin Mai na NNPC wanda da zarar komai ya kammala a watan Satumbar da muke ciki za’a fara ɗaukar man domin sayarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *