December 11, 2024

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

An Yi Kira Ga Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta Ɓaci Kan Ta’amali Da Miyagun Kwayoyi.

Daga Abdul’aziz Abdullahi

An bukaci Shugaban kasar Najeriya Bola Ahmad Tinubu,ya ayyana dokar ta ɓaci baci kan ta’amali da kwayoyi a ƙasar baki ɗaya.

Shugaban Gidauniyar Tallafawa Mabuƙata Daga Tushe wato Grassroot Care and Aid Foundation GCAF Amb Auwalu Muhammad Danlarabawa, ne ya yi kiran cikin wata takardar manema labarai da ya sanya wa hannu.

Auwalu Muhammad, ya ce akwai buƙatar a ayyana dokar ta bacin saboda yanzu lamarin yabkai dukkan masu aikata laifuka suna aikatawa ne sakamakon “shaye-shayen kwaya wanda ya haɗa da ta’adanci, kwacen waya, sace-sace, da Daba, da haukacewa kamar yadda ake ganin matasa da lananan yara harda nata akan titina duk sun haukace wasu suna kwana a titi da kuma dena zuwa makaranta”.

Shugaba Tinubu Ya Isa Brazil Taron G20.

Obasanjo Ya Nemi A Sauke Shugaban Hukumar Zaben Najeriya Mahmoodd Yakubu.

Kwankwaso Ya Yi Zargin Ana Neman Yi Musu Dole Daga Lagos A Harkar Masarautun Kano.

Ya kuma yi kira ga gwamnonin Arewa da su yi hakan suma kowanne ya ayyana dokar a jiharsa hakan zai taimaka matuka gaya “duba ga yadda kwaya ta cutar da rayuwar matasa a Arewa maza da mata yara da manya kuma lamarin na cigaba maimakon raguwa”, in ji shi.

A cewarsa “Matukar gwamnonin su ka bari aka cigaba da hakan to matsalar tsaro ba zata ragu ba, kullam laifika daban daban ne zasu dinga faruwa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *