December 11, 2024

Gwamnan Jigawa ya janye dakatarwar da ya yi wa kwamishinansa kan zargin lalata.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi, ya janye dakatarwar da ya yi wa kwamishinansa ayyuka na jihar Auwal Ɗanladi Sankara, bayan da wata kotu a jihar Kano ta wanke shi daga zargin aikata lalata.

Janye dakatarwar na kunshe ne cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Jigawa Bala Bala Ibrahim ya ake wa manema labarai a birnin Dutse.

Sanarwar ta ce, an janye dakatarwar ne biyo bayan wanke Kwamishinan daga zargin aikata lalata da wata babbar kotun shari’ar Muslunci ta yi a Kano.

Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Jigawa Ta Raba Tallafi Ga Al’ummar Kiyawa.

Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamiɗo Ya Caccaki Gwamnonin Arewacin Nijeriya Kan Zuwa Amurka.

An Yakenwa Wasu Mutum Biyu Hukuncin Ɗaurin Rai Da Rai A Jigawa Bayan Samunsu Da Laifin Yin Luwadi Da Wasu Yara.

Idan za a iya tunawa gwamna Namadi ya dakatar da Kwamishinan ne lokacin da hukumar Hisbah ta jihar Kano ta fara bincike kan wasu zarge zarge da ake masa domin bada damar yin bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *