December 11, 2024

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

ASUU ta nuna damuwa kan yawaitar ɗaliban da ke samun sakamakon first-class a Najeriya.

Daga Fatima Suleiman Shu’aibu

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU) ta bayyana damuwa kan yawaitar daliban da ke samun sakamako na farko (first-class) daga jami’o’in masu zaman kansu a Najeriya a kowace shekara, tana mai cewa wannan al’amari abin damuwa ne.

Daily Nigerian ta rawaito, Shugaban ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya bayyana wannan damuwa a ranar Alhamis yayin wani taron girmamawa da aka shirya don tunawa da nasarorin Farfesa Andy Egwunyenga a matsayin Mataimakin Shugaban Jami’ar Jihar Delta (DELSU).

NAHCON ta ce kowanne alhajin 2023 za a mayar masa da naira 60,080.

Shugaban Faransa ya yabawa Tinubu kan inganta ci gaban Najeriya.

Gwamnatin Najeriya za ta raba irin Alkama mai jure zafi ga manoma.

Farfesa Osodeke ya soki yadda jami’o’in masu zaman kansu ke bayar da lambobin yabo na sakamako na farko da yawa, yana cewa wannan dabi’a ka iya lalata nagartar ilimi idan jami’o’in gwamnati suka dauki wannan tsari ba tare da kyakkyawan tsari ba.

Har ila yau, ya yi karin bayani kan raguwar ingancin ilimi a matakin asali, yana ambaton makarantun firamare da sakandare da ke samar da dalibai da sakamako mai kyau amma ba tare da isasshen ilimi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *