Siyasa
Trending

Gwamna Abba Ya Rantsar Da Ɗan Kwankwaso A Matsayin Kwamishinan Matasa Da Wasanni.

Daga Ƙasiyuni Kamfa.

Gwamnan jihar Kano injiya Abba Kabir Yusuf, ya rantsar sabbin kwamishinoni guda 4 ciki har da ɗan gidan tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwas, wato Mustapha Rabi’u Kwankwaso a matsayin kwamishinan matasa da wasanni.

Sauran kwamishinonin sun hada da Adamu Aliyu Kibiya a matsayin sabon Kwamishinan kasuwanci sai kuma Abduljabbar Umar Garko Kwamishinan ma’aikatar ƙasa da safayo, inda Shehu Aliyu Yarmedi aka naɗa shi kwamishinan ayyuka na musamman.

Gwamnan ya kuma sauyawa Alhaji Abbas Sani Abba, ma’aikata zuwa Kwamishinan raya karka, Amina Abdullahi Sani HOD, ta koma Kwamishiniyar Jinƙan al’umma.

Kazalika Abba Kabir Yusuf ya rantsar da mataimaka na musamman da ya naɗa da kuma shugabannin hukumomi da manyan sakatarori.

Wakilin mu da ya halarci taron a fadar gwamnatin Kano ya rawaito cewa taron ya samu halartar manyan muƙarraban gwamnan da masu ruwa da tsaki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button