Siyasa
Trending

Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamiɗo Ya Caccaki Gwamnonin Arewacin Nijeriya Kan Zuwa Amurka.

Daga Fatima Sulaiman Shu’aibu

Tsohon Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido, ya caccaki Gwamnonin Arewacin Nijeriya da suka yi tafiya zuwa kasar Amurka taro kan tsaro, Lamido ya ce ziyarar tasu ta nuna rashin sanin makamar aikinsu.

A kwanakin baya ne, gwamnonin suka yi tattaki zuwa Amurka, inda suka halarci taron zaman lafiya da Cibiyar Zaman Lafiya ta Amurka ta shirya.

Da yake mayar da martani kan wannan kan zuwan nasu Amurka, a wani saƙo da Lamido, ya wallafa a shafin Facebook, ya ce tafiyar ta fallasa rashin gogewa da gwamnonin ke nunawa yayin da suke gudanar mulki.

Daga bisani Sule, yace idan da Gwamnonin sun yi tafiya zuwa Amurka don yin aiki kan yadda za a bunƙasa noma ko al’amurran kiwon lafiya ko wasu matsalolin gida da wannan zai iya zama mai amfani sosai ga al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button