Daga Abdul’aziz Abdullahi
A Najeriya hukumar kula da shige da fice ta ƙasar wato Nigeria Immigration Service (NIS) reshen jahar Gombe, ta yi ƙarin girma ga wasu jami’an ta domin ƙara ƙarfafa musu gwiwa akan ayyukan su.
Da ya ke jawabi a ya yin wani biki da ya gudana a dakin taro na sakatariyar gwamnatin tarayya da ke Gombe, a ranar Talata, controller janar na Hukumar Emmanuel Olayinka, ya shawarci jami’an da aka ƙarawa girman da su kasance masu biyayya ga hukumar tare da ba ta goyon baya a ayyukan da take don inganta shige da fice a ƙasar.
Gidauniyar OVPCF Ta Tube Shugabanta Na Bauchi, Tare Da Sallamarsa Baki Ɗaya.
Mohammed Salihu Al’amin na ɗaya daga cikin jami’an hukumar wanda ya samu ƙarin matsayi daga mataimakin sufuritanda na biyu zuwa na daya ya nuna farin cikin sa, in da ya ce hakan zai ƙara zaburar da su domin tabbatar da ayyukan su tafi yadda yakamata a faɗin ƙasar nan.