Tsaro
Trending

Jami’an Tsaro Sun Hallaka Ƴan Bindiga Da Kwato Makamai A Jihohin Kaduna Da Katsina.

Daga Mu’azu Abubakar Albarkawa

A Jihar Katsina ’yan sanda sun hallaka ’yan bindiga uku sun kuma ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su a yankin Gogalo da ke Karamar Hukumar Jibia.

Maharan sun shigo kauyen ne dauke da muggan makamai, inda suka sace mutum uku.

Daga bisani ’yan sanda suka bi sawu, suka hallaka uku daga cikinsu sannan suka kwato wadanda aka sacen.

A Jihar Kaduna, sojojin sun hallaka ’yan bindigar ne a yankin kananan hukumomin Kajuru da Birnin Gwari na jihar.

Sun kuma kama bindigogi kirar AK47 da sauran makamai da wayoyi, wasu kuma suka tsere da raunukan harbi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button