Tsaro
Trending

Hare-haren Da Isra'ila Ta Kai Cikin Dare Sun Kashe Aƙalla Mutum 55,- Hamas.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Wasu rahotanni sun ce, Hamas ta ce aƙalla mutum 55 ne suka mutu sakamakon hare-hare ta sama da Isra’ila ta ƙaddamar zuwa Gaza cikin dare, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

Ƙungiyar Ta ce fiye da gidaje 30 ne suka rushe a lokacin hare-haren.

Hakan na zuwa ne bayan da mai magana da yawun sojojin Isra’ila ya ce hare-hare ta sama a Zirin Gaza za su taimaka wa dakarunta da ke ƙasa, wajen tsara ƙaddamar da hare-hare.

Daniel Hagari, ya ce hare-haren za su taimaka wa Isra’ila rage wa dakarunta da ke ƙasa hatsari, wadanda ke jibge a kusa da kan iyaka.

Ya kuma yi kira ga fararen hular Falasdinawa da ke Gaza su ci gaba da ƙaura zuwa kudancin yankin, musamman waɗande ke zaune a birnin Gaza, domin kare lafiyarsu.

BBC ta ce, Isara’ila ta kuma kai wasu ƙarin munanan hare-hare ta sama zuwa Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da ta mamaye.

Inda hari na baya-bayan nan ya faɗa kan wani masallaci a Jenin, wanda sojoin Isra’ila suka zarga da zama ‘cibiyar ‘yan ta’adda”.

Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare a Gaza ne tun bayan da ƙungiyar Hamas ta kai mata hari a ranar 7 ga watan Oktoba da muke ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button