Jerin sunayen masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Najeriya da gwamnatin tarayya ta fitar
Tukur Mamu mawallafin Jaridar Desert Herald da ke Kaduna na daga cikin wanda gwamnatin ta ayyana
Hakan dai na ƙunshe cikin wata takarda da Hukumar Kula da Bayanan Sirri kan Harkokin Kuɗi ta Najeriya NFIU ta fitar a ranar Talata.
Ana iya tuna cewa, tun a watan Satumba na 2022 Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya DSS ta kama Tukur Mamu.
NFIU ta ce masu ɗaukar nauyin ta’ddancin da aka gano sun haɗa da waɗansu ’yan kasuwa tara masu zaman kansu da kuma wasu masu musayar kuɗaɗen ƙetare da aka fi sani da ‘yan canji guda shida.
Hukumar ta ce a wani taro da ta gudanar da yammacin ranar Litinin, ta ba da jerin sunayen mutanen tare da ba da shawarar gudanar da bincike a kansu.
NFIU ta ce Mamu ya taka rawa wajen samar wa da ‘yan ta’addda kuɗaɗe ta hanyar karba da kuma kai musu kuɗaɗen fansa hara dala dubu 200 da ke da alaƙa da mutanen da kungiyar ISWAP ta sace a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.
Sanarwar ta nakalto cewa, Antoni-Janar Lateef Fagbemi, tare da amincewar Shugaban Kasa Bola Tinubu ya sanya sunayen mutane da kamfanoni a cikin jerin waɗanda za a ƙaƙabawa takunkumi a Najeriya.
Daga cikin sauran mutanen, akwai wani mutum da ya kulla tare da samar da kuɗaɗen da aka yi amfani da su wajen kai harin ta’addancin da ya faru a Cocin St. Francis Catholic da ke Owo a Jihar Ondo da kuma harin da aka kai gidan gyaran hali na Kuje a ranar 5 ga watan Yulin 2022.
Akwai kuma wani mutum na daban da hukumar ta ce yana da alaka ta kud-da-kud da kungiyar ta’addanci ta Ansarul Muslimina Fi Biladissudan da ke da alaka da kungiyar Al-Qa’eda wadda ke aikinta a yankin Arewacin Afirka.
Bincike ya nuna cewa mutumin ya sami horo na musamman kan harkokin kuɗi da ta’adddanci karkashin wani mutum mai suna Mukhtar Belmokhtar, wanda aka fi sani da “Mai ido daya” shugaban kungiyar Al-Murabtoun Katibat ta AQIM da ke gudanar da ayyukan ta’addanci a kasashen Algeria da Mali.
NFIU ta kuma ce wannan mutum dai shi ne mai tsaron lafiyar jagoran kungiyar Boko Haram tsagin Ansaru, Mohammed Usman wanda aka fi sani Khalid Al-Bamawi.
Hukumar ta ce waɗannan mutane sun kware wajen tsarawa da kuma samar da kudaden da za a yi amfani da su wajen kai hari, da kuma shiga tsakanin kungiyoyin ta’addanci da masu taimaka musu wajen kera makamai musamman bama-bamai.
Kazalika, akwai wani mutum da ke da alaƙa ta kai-tsaye kan harkokin kudade da kungiyar IS ta yammacin Afirka da ke Okene.
Hukumar ta ce mutanen sun fara alaƙa ta kai-tsaye da kungiyar Boko Haram a 2012, inda kuma daga baya suka zama masu shiga tsakani wajen kulla yadda za a kai hare-hare ko kuma samar da kuɗaɗe.