"Ka Mayar Da Hankalinka Kan Aikinka, Ka Kyaleni," Cewar Matawalle Ga Gwamnan Zamfara.
Daga Firdausi Ibrahim Bakondi
Karamin Ministan Tsaro, Dakta Bello Matawalle, ya shawarci Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara da ya mayar da hankali kan aikinsa na mulkin jihar.
Matawalle ya ba da wannan shawarar ne a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a birnin Abuja.
Inda ya mai da martani kan wasu zarge-zargen da Dauda ya yi masa a lokacin da ya ke matsayin gwamnan jihar.
Zargin da ake masa ya shafi almubazzaranci da dukiyar al’umma, cin basussuka masu yawa da kuma rashin biyan kudin jarabawa da kudin makaranta na dalibai a gida da waje, da dai sauransu.
“Ina ganin mutumin bai shirya yin mulki ba, a kullum sai zarge-zarge a maimakon ya tattara hankalinsa ya kuma tabbatar da cewa ya samar da dimokuradiyya ga al’ummar Zamfara”, in Matawalle.
Matawalle ya bayyana cewa Dauda yakan yi fada ne kawai gami da waiwaye kan abin da ya faru a baya , yace gwamnoni kusan 4 ko 5 ne sukayi mulki a bayan sa kuma dukkanin su babu wanda ya wai wayi abinda dan uwansa yayi daga cikinsu, yace a maimakon Dauda ya maida hankali kan sha’anin tsaro da jihar da ake bukata, sai kawai ya koma zargi, a cewar Matawalle.
Matawalle ya kara da cewa Lokacin da aka yi garkuwa da daliban Jami’ar Gusau, Shugaban kasa ya umurci dukkan gwamnoni da jami’an tsaro da suje wurin don jajantawa al’ummar jihar da kuma iyayen daluban.
Yace Dauda ya bar cikin jihar, Ya tafi kasar waje yace sun kirashi kuma bai dauka ba, yace sai da sukabi ta wani bangare kafin suka samu wani lamba suka kirashi.
Kana alokacin ne ya roki Ministan , cewa ba ya nan, amma da zarar ya dawo, zai sanarda su , inda kuma suka bayyana masa cewa wannan tawaga ce da shugaban kasa ya ba da umarnin zuwa jihar sa domin jajanta wa iyayen daliban da aka sace.
Yace Dauda yana zargin sa ne kawai babu dalili, “kamata ya yi ya maida hankalinsa kan aikinsa, an zabe shi ne domin tunkarar al’amuran jiharsa”.
Matawalle yace a matsayinsa na magabacin Dauda, a ko yaushe yana masa addu’ar samun nasara, wajen tabbatar da cewa batun rashin tsaro, ta’addanci da ‘yan fashi sun zama tarihi a jihar.
Ya jaddada cewa ko min yaya shima jiharsa ce, iyalansa da duk yan uwansa suna jihar, “a kullum ina ddu’ar Allah ya ‘yanta mu kuma ya tsare mu daga irin wannan yanayi”, in ji shi.