Notice: Constant DISALLOW_FILE_EDIT already defined in /home/martabaf/public_html/wp-config.php on line 98
Kotu ta bayar da umarnin karɓe dalar Amurka miliyan 1.4 daga Emefiele - Martaba FM Kotu ta bayar da umarnin karɓe dalar Amurka miliyan 1.4 daga Emefiele - Martaba FM

Mai Shari’a Ayokunle Faji na Babbar Kotun Tarayya da ke Legas, ya ba da umarnin ƙarshe na karɓe dala miliyan 1.4 da aka danganta da tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele, domin mayarwa Gwamnatin Tarayya.

A baya, alkalin kotun ya ba da umarnin ƙarshe na karɓe kuɗin a ranar 24 ga watan Yuni 2024, amma ya soke shi a ranar 27 ga watan Yuni 2024, bayan waɗanda abin ya shafa suka ƙalubalanci hukuncin.

Daga baya, kotun ta umarci waɗanda suka shigar da ƙara da su gabatar da hujja da ke nuna dalilin da ya sa bai kamata a karɓi kuɗin ba, tare da ba Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) damar sake gabatar da ƙarar.

Masu ƙarar sun musanta sanin asalin kuɗin, in da suka ce ba su da wata masaniya game da su kuma kuɗin ba su fito daga wata haramtacciyar hanya ba.

Sai dai a hukuncin sa na ranar Alhamis, Mai Shari’a Faji ya tabbatar da umarnin karɓe dala miliyan 1.4, ya na mai cewa EFCC ta tabbatar da cewa kuɗin an samo su ne ta haramtacciyar hanya.

By Moddibo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *