Daga Suleman Ibrahim Modibbo
A aƙalli sama ɗalibai 12,000 suka nuna sha’awarsu ta zama ɗaliban jami’ar Yusuf Maitama Sule, da ke birnin Kano a Arewacin Najeriya a shekarar 2024.
An rubuta jarrabawar ta POST UTME ce a ranar Asabar ɗin makon jiya a makarantar ƙarƙashin jagorancin shugaban Jami’ar Farfesa Mukhtar Kurawa.
Da ya ke zantawa da manema labarai Farfesa Mukhtar Kurawa, ya ce sun gamsu da yadda aka gudanar da jarrabawar cikin yanayi mai kyau, “sama da mutun 12,000 ne su ka zauna”.
Sai da kuma ya ce cikin ɗalibai sama dubu 12 da suka rubuta jarrabawar mutum 6,000 kaɗai makarantar za ta iya ɗauka “abun da hukuma ta sahale mana mu ɗauka shine 6,000 don haka ba mu da yadda za mu yi face a tantance ta wannan hanyar.
“A baya ba ma wuce ɗalibai 5,000 amma yanzu bisa sake ƙara wasu fannoni da mu kai a jami’ar kullun sake samun ƙarin damar ɗaukar dalibai mu ke yi”, in ji shi.
Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa ya raba Babura dubu 1 ga Ƴansandan Kano.
Kano Pro-pa ta nemi Gwamnatin Kano ta tsayar da ginin wasu ajujuwan karatu.
Kwankwaso Ya Yi Zargin Ana Neman Yi Musu Dole Daga Lagos A Harkar Masarautun Kano.
Farfesa Kurawa ya roƙi masu hannu da shuni da su ci gaba da tallafawa jami’ar don yin gogayya da na ƙasashen waje.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
“Kwararar masu aikata laifuka daga jihohin makwabta ne abin da ya taimaka wajen ƙalubalen tsaro”- Gwamnatin Gombe.
-
Kano da Katsina, sun zama a sahun gaba wajen matsalar rashin isassun takardun kuɗi.
-
Kamfanin Turkiyya zai fara haɓaka noman zamani a Zamfara.
-
Ƙungiyar Alkalai sun shiga yajin aikin sai baba ta gani.
-
NAFDAC ta gargaɗi masu gidajen Burodi kan amfani da Sakarin.