December 9, 2024

Tinubu Ya Gaji Gwamnati Wadda Ta Talauce- Rabadu.

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya ce shugaban Najierya Tinubu ya gaji gwamnati wadda ta talauce, sa’ilin da yake magana kan matsalar kudin da ƙasar ke fama da ita.

Ribadu, wanda ya amince cewar akwai matsaloli a ɓangaren kuɗi na ƙasar, ya ce duk da waɗannan kalubalen, gwamnatin tarayya ta himmatu wajen tabbatar da ingantaccen tsarin kula da tsaro a kasar.

BBC ta rawaito, Ribadu ya faɗi hakan ne a taron shekara-shekara na shugaban sashen tattara bayanan sirri na 2023 a Abuja, mai taken “Yin amfani da diflomasiya na tsaro da ingantaccen haɗin kan yanki don Inganta tsaron ƙasa,”.

Ribadu ya jaddada sadaukarwar gwamnati ga tsaron ƙasa.

Taron ya samu halartar manyan baƙi da suka hada da ministan tsaro, Abubakar Badaru, da babban sakatare Ibrahim Kana, da babban hafsan soji, tare da wasu hafsoshin tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *