LabaraiLafiya
Trending

Cutar Kyanda Ta Kashe Ƙananan Yara 19 A Jihar Adamawa.

Daga Fatima Suleiman Shu’aibu

A kalla yara kanana 19 ne suka rasu sanadiyyar kamuwa da cutar Kyanda  a karamar hukumar Mubi, dake  Jihar Adamawa.

Kwamishinan lafiya na jihar Felix Tangwami ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a Mubi ranar Asabar cewa sama da yara 200 ne suka kamu da cutar a karamar hukumar.

Ya ce an soma samun labarin barkewar cutar ce a garin Yola, inda cikin gaggawa aka tura jami’an lafiya da magunguna domin a taro cutar kada ta yi ɓarkewar da ba za a iya shawo kansa da wuri ba.

Ya kuma ba da tabbacin cewa za a mika yaran da suka kamu da cutar zuwa snyan asibitocin jihar domin a basu kulawa.

Premium Times ta ruwaito cewa Kwamishinan ya ce tawagar likitocin za su kuma nausa zuwa karamar hukumar Gombi inda aka sake samun bullar cutar.

A karshe Tangwami ya dora laifin kin kai yara asibiti a yi wa ‘ya’ya rigakafin citar tun farko ne yi sanadiyar samun ɓarkewar cutar a yankunan jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button