Labarai
Trending

Sheikh Yusuf Ali Ya Yi Tasiri Ga Ɗimbin Jama'a A Tsawon Rayuwarsa- Tinubu.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Shugaba ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhininsa kan rasuwar babban malamin addinin Musulunci da ke jihar Kano, Sheikh Yusuf Ali, wanda ya rasu a safiyar ranar Litinin.

Shugaban ya aike da sakon alhini zuwa ga iyalai, dalibai, da kuma mabiya wannan malami da ke Kano, da ma Masarautar Gaya wanda wannan malami ke kan karagar sarkin malamanta a lokacin rayuwarsa.

Cikin wata sanarwar da mai taimakawa shugaban ƙasar kan harkokin yaɗa labarai Ajuri Ngelale ya fi fitar a ranar Litinin ta ce Shugaba Tinubu ya bayyana rasuwar jagoran addinin a matsayin wani babban abun alhinin da ya karade muryoyin jama’a a fadin kasar nan, duba da irin dimbin mabiyan da marigayin ke da shi musamman ma mabiyan darikar Tijjaniyya a ciki da wajen Najeriya.

“A matsayinsa na mai koyarwa, sha’iri, masanin shari’ar musulunci da tsirrai, kuma uwa uba malamin addinin Islama, Sheikh Yusuf Ali ya yi tasiri ga dimbin jama’a a tsawon rayuwarsa wadda ya sadaukar da ita kacokan wajen neman ilimi da yada shi” in ji shugaban.

Manyan Ayyuka Biyu Da Za Su Kai Shugaba Tinubu Ƙasar Saudiyya.

Shugaba Tinubu ya mika ta’aziyyarsa ga iyalai da almajiran marigayin da kuma gwamnatin jahar Kano da al’ummar jihar da ma daukacin Musulmin Najeriya bisa wannan rashi da aka yi ya na mai addu’ar Allah ya jikan Malamin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button