Notice: Constant DISALLOW_FILE_EDIT already defined in /home/martabaf/public_html/wp-config.php on line 98
Tsadar Rayuwa: Ba Da Daɗewa Ba Abubuwa Za Su Yi Kyau -Gwamnatin Najeriya. - Martaba FM Tsadar Rayuwa: Ba Da Daɗewa Ba Abubuwa Za Su Yi Kyau -Gwamnatin Najeriya. - Martaba FM

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Litinin, ya amince cewa ‘yan Najeriya na fuskantar matsaloli, amma ya ba da tabbacin cewa nan ba da daɗewa ba lamarin zai sauya da kyau.

Yayin da Tinubu ya nanata cewa gwamnatinsa na kan hanya, ya kuma lura cewa mafita ga al’amuran da ke faruwa ba za su kasance cikin gaggawa ba.

Daily Trust ta rawaito cewa, Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a wajen taron bikin cika shekaru 70 na Shugaban Citadel Global Community, Fasto Tunde Bakare a Legas, wanda
Sakataren Gwamnatin Tarayya Sanata George Akume da Gwamnan Legas suka wakilce shi.

A nasa bangaren, gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana waɗanda ke shugabanci a mulkin Najeriya a matsayin jajirtattun mutane da ke ƙoƙarin ganin an shawo kan matsalolin da ake fama da su.

By Moddibo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *