Tsaro
Trending

Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 A Benue.

Daga Firdausi Ibrahim Bakwandi

Akalla mutane 10 ne aka kashe a tsakanin ranakun Asabar da Lahadi a hare-haren da aka kai a kan hanyar Ayilamo zuwa Anyin da kuma al’ummar Chembe da ke karamar hukumar Logo ta jihar Benue.

Daily Trust ta rawaito, da yake tabbatar da aukuwar lamarin kakakin ƙaramar hukumar Logo Paul Pevikya, ya ce, kisan ya zama ruwan dare gama gari, kuma yana bakin cikin bayyana cewa wasu makiyaya dauke da makamai sun kashe sama da mutane 10 a karshen mako da ya gabata.

An bayyana cewa daya daga cikin waɗanda abin ya shafa daliba ce a Jalingo na jihar Taraba wanda suka afka mata a daren ranar asabar din da ta gabata.

Dan uwan wanda abin ya faru da ita ya bayyana cewa, yaji lokacin da yar uwarsa take kiransa inda kafin ya isa inda take maharan sun kashe ta.

Manema labarai sunyi ta kokarin zanta da Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Benue , SP Catherine Anene, kan lamarin amma abu yaci tura.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button