Labarai
Trending

Ƴan Sanda Sun Sha Alwashin Farauto Waɗanda Suka Kashe Shugaban YPP A Jihar Anambra.

Daga Firdausi Ibrahim Bakwandi

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Anambra, CP Aderemi Adeoye, ya sha alwashin cewa rundunar za ta farauto waɗanda ake zargin sun kashe shugaban jam’iyyar Young Progressive Party (YPP) a mazaɓar Nanka Ward da ke karamar hukumar Orumba ta Kudu.

Komishinan wanda ya yi Allah wadai da kisan, yana bayyana wadanda suka yi kisan a matsayin matsorata tunda suka kashe wadan da suke barci, ya kara da cewa za su yi dukkanin mai yuyuwa wajen kawo waɗanda suka aikata laifi gami da gurfanar da su a gaban kuliya.

“Yace za su yi tunanin sun sha kan laifun da suka aikata, amma ya ce doka za ta yi aiki akansu”, in ji shi.

Adeoye ya ce tuni ‘yan sanda suka fara aiki da wasu muhimman bayanai domin bankaɗo masu laifin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button