Ƴan Kasuwar Man Fetur Sun Fara Siyen Man Daga Matatar Dangote.

Yayin da ƴan Najeriya ke ci gaba da shan man fetur da tsada, matatar man Dangote ta fara sayar da man fetur ɗin kai-tseye ga ‘yan kasuwa bayan janyewar dillancin man da babban kamfanin mai na ƙasar NNPCL ya yi.

BBC ta ce, ƴan kasuwar da dama – waɗanda suka jima suna shigo da man daga ƙetare – sun zaƙu a fara sayar musu da man kai-tseye daga matatar ba tare da wani mai dillanci a tsakiya ba.

Zancen Man Fetur Ya Sauka Zai Yi Wahala, -Ɗangote.

Muna Roƙon Gwamnatin Najeriya Ta Dawo Da Tallafin Man Fetur,- Sheikh Qaribullah.

Sojin Saman Najeriya Sun Kashe Ƴan Bindiga A Dazukan Kaduna Da Zamfara.

A makonnin da suka gabata ne dai babban kamfanin mai na ƙasar, NNPCL ya sanar da janyewa daga dillancin man na Dangote, domin bai wa ‘yan kasuwar damar sayen man kai-tseye daga matatar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Proudly powered by WordPress | Theme : News Elementor by BlazeThemes