Labarai
Trending

Sama Da Ɗalibai Miliyan 1.2 Ne Suka Amfana Da Gyara Da Faɗaɗa Makarantun Sakandare A Jihar Kano.

Sama Da Ɗalibai Miliyan 1.2 Ne Suka Amfana Da Gyara Da Faɗaɗa Makarantun Sakandare A Jihar Kano.

Daga Sadik Muhammad Fagge

Shirin AGILE Kano yana samun ci gaba wajen inganta ilimin yara mata masu tasowa a yankuna birni da karkara .

Babban Jami’in dake kula da ayyukan AGILE a jihar Kano Nasir Abdullahi Kwalli shine ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a kano.

Nasir Kwalli ya ce babban makasudin shirin shi ne magance matsalolin da suka addabi makarantun Sakandare, musamman ga yara mata, wadanda dayawansu ke fuskantar matsaloli kamar rashin isassun makarantu a yankunansu, kayayyakin more rayuwa, ruwa,da tsaftar muhalli.

Yace Idan har da gaske kuke son ganin an samu ci gaba a cikin al’umma, to sai kun fara da tarbiyyar ‘yan mata domin su ne uwayen gobe, idan kuna da dimbin ‘yan mata masu ilimi za a samu sauki wajen yada Ilimi ga kowa da kowa.

Domin cimma wannan buri, kungiyar AGILE Kano Project ta fara daukar matakai kai tsaye, kamar gina sabbin kananan makarantu da manyan makarantun gaba da sakandare a yankunan karkara a Kano, samar da ruwan sha da gina bandakai ga ‘yan mata a makarantun sakandare, da baiwa makarantu tallafi da gyara abubuwan more rayuwa da suka lalace.

A cewar Kwalli, Izuwa yanzu an gyara makarantun sakandire 1,228 kuma ana ci gaba da kirgawa.

Ya kuma ce kimanin dalibai 1,269,673 ne suka amfana kai tsaye daga aikin AGILE kuma Ana kan fadada aikin.

“Babu wata al’umma a Kano da ba za ka iya samun aikin AGILE ba, kuma wannan shi ne mafari, wannan kadan ne, da yawa kuma suna tafe nan ba da dadewa ba.” Inji Nasir kwalli.

Bankin Duniya ne ke daukar nauyin shirin na AGILE Kano, kuma Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano tare da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki ne ke aiwatar da shi.

Wannan aiki dai na da nufin kara samun daidaiton ilimin makarantun gaba da sakandire tare da inganta karatun da rikon amana a makarantun sakandaren jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button