Dan Majalisar Tarayya A Fagge, MB Shehu ya Raba Tallafin Naira Miliyan 5 Ga Yan Jam’iyyar NNPP.
Daga Sadiq Muhammad Fagge
Dan majalisar wakilai mai wakiltar karamar hukumar Fagge a jihar Kano, Muhammad Bello Shehu, ya raba Naira miliyan biyar ga magoya bayan jam’iyyar sa ta NNPP a matsayin tallafi dogaro da kai.
Dan majalisar wanda aka fi sani da MB Shehu, da yake jawabi a lokacin da yake raba kudaden a wani taron da aka gudanar a karamar hukumar Fagge a ranar Juma’a, ya ce ya yi hakan ne domin tallafa musu ta yadda za su inganta kasuwancinsu da kuma sana’o’in da suke da yi.
A cewarsa, an raba musu kudaden ne domin nuna godiya bisa ga goyon baya da gudunmuwar da suka bayar har jam’iyyar NNPP ta sami nasarar a zaɓukan da aka gudanar a shekarar 2023.
Mb shehu, ya bayyana cewa, 16 daga cikin waɗanda suka ci gajiyar shirin za a ba su Naira 200,000 kowanne, yayin da 7 daga cikinsu za su samu Naira 100,000 kowannen su, mutane 20 kuma kowanne su zai samu N50,000.
Ya kara da cewa shirin tallafin wanda aka kaddamar a ranar Juma’a a mazabu biyu na Fagge (A) da Yanmata Gabas zai ci gaba da gudana duk wata.
Dan majalisar ya bayyana cewa ya raba kudaden ne ga wadanda suka ci gajiyar shirin daga cikin albashin da yake karba na wata-wata, wanda a cewar sa, za a ci gaba da daukar mazaɓu guda biyu a kowane wata har zuwa watan Disamba na wannan shekara.
“Wannan ba ya daga cikin aiyukan mazaɓu, tallafi ne daga cikin albashina na wata-wata a matsayina na dan majalisa naga ya dace na tallafa wa waɗanda suka yi aiki tukuru tare da tallafa mana wajen samun nasarar zabenmu.
“Sun cancanci fiye da wannan, saboda wadannan mutanen su ne suka sha rana suka sha wuya, kuma sun fuskanci cin zarafi daga yan adawa kala-kala har Allah ya bamu nasara don haka ya zama wajibi mu tallafa musu”, a cewar MB Shehu.
MB Shehu ya kuma ce ya tanadi ayyuka da dama ga al’ummar karamar hukumar Fagge, inda ya bayyana cewa zai fito da managartan tsare-tsare na taimaka wa al’ummar sa, ta yaddada sauran ‘yan majalisu za su rika yin koyi da shin nan da ‘yan watanni masu zuwa.
Tun da farko a nasa jawabin, wani na hannun damar majalisar, Mustapha Isa, ya ce MB Shehu yana da kishin mutanensa don haka yake gudanar da ayyukan da za su inganta rayuwar al’ummarsa.
Ya kuma tabbatar wa da al’ummar Fagge cewa za su cigaba da ganin ayyukan raya kasa da inganta rayuwar al’umma don cigaban karamar hukumar Fagge ta fuskar tattalin arziki da dai sauransu.