Siyasa
Trending

An Ɗage Zaman Shari'ar Cin Hanci Da Aka Fara Yi Wa Ganduje A Kano Zuwa Wata Rana.

Babbar Kotun jihar Kano mai lamba 4 ƙarƙashin mai Shari’a Usman Na’abba ta soma sauraron ƙarar da Gwamnatin Kano ta shigar da Tsohon Gwamna Ganduje da wasu mutane.

Freedom Radio mai yaɗa shirye-shirye a jihar Kano ya rawaito cewa, yayin zaman Kotun lauyoyin waɗanda ake ƙara sun bayyanawa Kotun cewar masu ƙara ba su shirya ba domin sun gaza sadar da sammaci ga waɗanda ake ƙara duk da shari’ar ta laifi ce.

A nan ne lauyoyin Gwamnati suka roƙi Kotun ta yi umarni da wadanda ake ƙara su zo gabanta, sai dai Lauyan masu kariya roki kotu ta yi watsi da rokon inda ya ce irin wannan shari’ar sammaci kawai ake kai wa ba sai Kotu ta ba da umarni ba.

A ƙarshe Kotun ta sanya ranar 29 ga watan Afrilun da muke ciki domin ci gaba da shari’ar.

Gwamnatin Kano ta hannun Hukumar Yaƙi da Rashawa ta Kano ce ta yi ƙarar Tsohon Gwamnan da wasu mutane ciki har da matarsa da ɗansa bisa zargin sayar da kadarorin Gwamnati ba bisa ƙa’ida ba, da wadaƙa da dukiyar jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button