Siyasa
Trending

Atiku Ya Koka Da Ƙarin Kuɗin Wutar Lantarki Da Gwamnatin Tinubu Ta Yi Wa Ƴan Najeriya.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya Atiku Abubakar, ya koka da ƙarin kuɗin wutar lantarki da gwamnatin Tinubu ta yi wa ƴan ƙasar.

Gwamnatin Najeriya ta amince da ƙara kuɗin wutar lantarki nan take daga ₦66 zuwa ₦225 kan kowane kilowatt ɗaya ga masu samun wutar awa 20 a rana.

Tun a ranar farko ta kama mulkin shugaba Tinubu, ne ya janye tallafin Man Fetur da kuma kawo sauye-sauye ga bangaren taltalin arziƙin ƙasar, wanda hakan ya haifar da tashin kayyaki da tsadar rayuwa da ta sanya ƴan ƙasar cikin matsi.

Atiku Abubakar wanda shine jagoran ƴan Adawa a Najeriya kuma shine ya yi wa jam’iyyar PDP takarar shugaban ƙasa a zaɓen da ya gabata ya yi zargin cewa gwamnatin Tinubu tana sane take gasawa ƴan ƙasar ƙasa aya hannu abinda ke jigata su.

“Kamar yadda gwamnatin ta saba, a wannan karon ta sake ɓullo da Wani tsari mai tsauri ba tare da wani wa’adi ko samar da wasu tsare-tsaren rage raɗaɗin da matakin zai haifar ba”, in ji Atiku.

“Ƙarin Farashin kuɗin lantarki ya zo wa ‘yan Najeriya a daidai lokacin da suke kan ɗanɗana kuɗar su sakamakon janye tallafin man Fetur da kuma rugujewar darajar Naira.”

A cewar sa, “gwamnatin ba ta iya shawo kan matsalolin da suka biyo bayan aiwatar da waɗancan manufofin ba, kuma yanzu ta bujuro da wani sabon tsarin na ƙarin kuɗin wuta da zai kyankyashe sababbin matsaloli ga ‘yan kasa domin zai ƙara haifar da tsadar kayayyaki.”

“Ɓangaren masana’antun mu abin zai shafe su sosai, bawai kawai biyan basukan da suka ci a bankuna ba wanda zai ƙara yawa yanzu akwai kashe kudi mai yawa wajen siyan Disel da biyan albashi mai yawa sakamakon sabon mafi ƙarancin albashi, waɗanda suka kewaye shugaban kasa suna ƙara jefa tattalin arzikin ƙasa cikin mummunan yanayi, manufofin sa babu tunanin talakawa a ciki.”

Yana da mutuƙar muhimmanci mu fahimci mene ne ke haddasa matsaloli a ɓangaren wutar lantarki kafin kawo irin wannan manufa, Lokaci ya yi da za a waiwayi yadda aka bi wajen sayar da ɓangaren wuta har aka haifar da kamfononin DISCOs”.

“Wajibi ne Tinubu na farko ya tabbatar waɗannan tsare-tsaren an Yi su kan tsari, na biyu a aiwatar da shirin da zai rage raɗaɗin matakan ga yan Najeriya, Sannan na uku a tabbatar an ɗorawa hukumar NERC alhakin tabbatar da ganin komai ya tafi daidai wurin Samar da lantarkin”, in ji Atiku Abubakar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button