Labarai
Trending

Direwa Ya Kashe Mutum Biyo A Jihar Legas A Ƙoƙarin Na Tserewa Jami'an LASTMA.

Daga Firdausi Ibrahim Bakwandi

Rahotanni daga jihar Legas a kudancin Najeriya, sun bayyana cewa wani direba ya kashe wasu mutum biyu da ke tsaftace tituna yayin da yake kokarin tsere wa jami’an LASTMA.

Daliy Trust ta rawaito cewa, a ranar Litinin din da ta gabata ne wani direba ya kashe wasu masu aikin tsaftace titi guda biyu a lokacin da yake kokarin tserewa wani samame da jami’an hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa na jihar Legas suka kai musu.

Wani ganau ya bayyana cewa an dade ana irin wannan abu da suka kirashi da cin zarafi da muguntar Gwamnatin Jihar Legas da Hukumar LASTMA ke yi, sun kuma buƙaci da a kawo karshen muzgunawar da ake nunawa.

“Duba abin da ya faru, ‘yan uwa biyu sun mutu saboda wani jami’in LASTMA yana bin wata motar bas.

Kazalika an bayyana cewa masu tsaftace titunan na zargin gwamnatin jihar da jefa rayuwar al’uma cikin hatsari.

Daga baya an yi zanga-zangar nuna adawa da ayyukan LASTMA a tashar mota ta Ile Zik da ke kusa da yankin Ikeja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button