LabaraiLafiya
Trending

Majalisar Dokokin jihar kano ta amince da dokar yin gwajin cutar Ƙanjamau da Sikila da wasu cututtuka kafin aure

Majalisar Dokokin jihar kano ta amince da dokar yin gwajin cutar kanjamau da ta Sikila da kuma sauran cututtuka kafin yin aure.

Da yake Jawabi akan kafa dokar, Shugaban Majalisar dokokin jahar kano Alhaji Jibril Isma’il Falgore, ya ce dokar za ta daƙile yaɗuwar cututtuka a tsakanin ma’aurata da yaɗa su ga iyali da ma al’umma baki ɗaya.

Haka zalika dokar ta ba da damar yin gwajin cututtuka masu haɗari da wuyar magani kafin yin aure, tare da tanadin hukunci mai tsanani ga duk wanda yaƙi yin biyayya ga dokar.

Mataimakin Akawun Majalisar kuma babban Sakatare Alhaji Nasiru Magaji, ne ya gabatar da karatu na uku akan dokar kafin amincewa da ita a ranar Litinin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button