Ilimi
Trending

Ɗaruruwan Ƴan Ƙaramar Hukumar Dala Za Su Amfana Da Ilmin Kwamfuta A Kyauta.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

An ƙaddamar da wani kwamitin lura da horar da matasa maza da mata kan ilimin kwamfuta a ƙaramar hukumar Dala da ke jihar Kano a Arewacin Najeriya, wanda gidauniyar AB Muƙaddam Foundation, ta sada shiryawa lokaci zuwa lokaci a ƙaramar hukumar.

Yayin wani ƙwarya-ƙwaryan bikin da gidauniyar ta shirya a ofishin sakataren Ilimi na ƙaramar hukumar Dala aka ƙaddamar da shirin, wanda ya samu halartar masu gudanar da shirin bisa jagoranci Honorable Abba Bala Dala, wani matashi ɗan jam’iyyar APC a jihar Kano.

Da yake jawabi shugaban gidauniyar AB Muƙaddam, Abba Bala Dala, ya ce, suna shirya horon ne kan kwamfuta saboda matasa masu tasowa su fahimci yadda ake sarrafa kwamfutar “la’akari da mahimmancin ta wajen gudanar da rayuwar yau da kullum, da yadda ta zama hanya mafi sauƙi ta samar da aikin yi ga matasa” in ji shi.

Credit/AB Muƙaddam
Sakataren Ilimi na Dala Hamidu Abdullahi tare da Abba Bala Dala lokacin da yake miƙa masa sheda.

Malam Hamidu Abdullahi, wanda shine Sakataren Ilimi na ƙaramar hukumar Dala, ya hori ƴan kwamitin lura da shirin su zama masu kwazo da nagarta a lokacin gudanar da shirin, wanda ya ce yana da mahimmanci ga ƙaramar hukumar Dala da jihar Kano.

Hamidu ya kuma yabawa shugaban gidauniyar Abba Bala Dala, bisa irin ƙoƙarin da yake yi na bayar da ilimi kyauta ga matasan Dala, wanda ya ce ta haka ne kaɗai za a ƙara samun al’umma mai ilimi ƙaramar hukumar.

Za a buɗe bayar da Form na shiga shirin ne a ranar Laraba 18 ga watan Oktoba na wannan shekara ta 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button