Akwai Buƙatar Al’ummar Kano Su Shiga Fafutukar Yaƙi Da Sauyin Yanayi- ACRESAL Kano.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Shugaban shirin Alkinta Muhalli da Yaƙi da Sauyin Yanayi na Bankin Duniya wato ACRESAL a jihar Kano Dr.Ɗahiru Muhammad Hashim, ya buƙaci al’umma jihar musamman matasa, su shiga fafutukar yaƙi da sauyin yanayi da inganta muhalli.

Dr.Ɗahiru ya bayyana haka ne cikin wani shirin kai tsaye da aka yi da shi a shafin Martaba FM na Facebook da tsakar ranar Lahadi.

Ya ce yaƙi da sauyin yanayi abu ne da yake wuyan kowa, “yawaici wannan abubuwan da muke yi abu ne wanda gwamnati kaɗai ba za ta iya ba, kowa sai ya ba da tasa gudummawar sanan ake samun al’umma mai inganci da kowa yake fata”.

Ya ƙara da cewar ya kamata matasa su ɗauki gabarar ayyukan dashen bishiyoyi, “ko wani matashi bai wuce ya sayi bishiya guda ɗaya ba, ko ya nemo ya dasa, irin waɗannan abubuwan sune muke so matasan mu su fahimta”, in ji Dr.Ɗahiru.

“Yawaici sauyin yanayin nan mune muke fuskantar ƙalubalen sa fiye da kowa, saboda mune muk sa ran za mu ƙara shekaru nan gaba, matsalolin mu suka shafa, duka matsalolin suna gurɓata muhalli”.

A cewar sa, suna ba ƙungiyoyi da ɗai ɗai ku damar su yi aiki da su, “ko a baya mun raba kayayyakin aiki ga ƙungiyoyi na ƙananan hukumomi”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Proudly powered by WordPress | Theme : News Elementor by BlazeThemes