Labarai
Trending

An Kafa Hukumar Tsare-tsaren Taltalin Arziki A Jihar Jigawa.

Daga Sadik Muhammdad Fagge da Firdausi Ibrahim Bakwandi.

Gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi, ya kaddamar da hukumar tsare-tsaren tattalin arziki ta jihar wato (EPB) a turance, wanda hakan ke nuna gagarumin ci gaba na bunkasa tsare-tsare da ci gaban tattalin arzikin jihar.

Cikin wata sanarwa da Hamisu Mohammed Gumel, babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar ya fitar a ranar Litinin ta ce, kafa hukumar ya kasance daidai da doka mai lamba 8 ta shekaran 2016, wanda wani muhimmin aiki ne da ya samo asali daga sashe na 7 karamin sashi na (3) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya, na shekaran 1999.

“Hukumar Tsare-tsaren Tattalin Arziki ta samo asali ne tun lokacin da aka kafa dokar hukumar EPB a cikin shekara ta 2000, duk da kasancewarta doka ta fuskanci ƙalubale da suka kai ga soke ta a shekarar 2012 duk da haka, tasirinta ya kasance mai ɗorewa, wanda ya haifar da ƙirƙirar tsare-tsare, bincike da sassan kididdiga a kananan hukumomi da kuma amincewa da dabarun karfafa tattalin arziki da ci gaban kananan hukumomi, tare da yin gyara ga dokar kananan hukumomin jihar Jigawa”, in ji sanarwar.

Sanarwar ta kuma ce an sake aiwatar da dokar hukumar EPB a cikin shekara ta 2016 tare da sabunta mayar da hankali kan tabbatar da ingantaccen aiki, wanda suka hada da tantancewa da ba da shawarari kan manufofin ci gaba ga jihohi da kananan hukumomi, daidaita aiwatar da su, samar da abubuwan da suka dace a cikin tsare-tsaren raya kasa, nazarin daidaiton kasafin kudi, da kula da kudaden ayyukan ta hanyar asusun hadin gwiwa na gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi.

“An dora wa kwamitin ayyuka da dama, wanda suka hada da bayar da shawarwari kan manufofin raya kasa, bayar da shawarwari kan tsare-tsaren raya kasa, tabbatar da daidaiton kasafin kudi, yin nazari da daukar matakai kan rahotanni aiwatar da kasafin kudi, amincewa da ayyukan da za a yi don samar da kudade, lura da bin doka da oda, sanya ido kan ababen da suka dace, gami da rabon ayyuka a fadin jihar”, in ji shi.

Gwamna Umar Namadi ya karbi mukamin shugaba, inda mataimakinsa ya kasance a matsayin mataimakin shugaban kwamitin, sauran mambobin sun hada da sakataren gwamnatin jiha, kwamishinonin manyan ma’aikatu, mai bai wa gwamna shawara na musamman kan kasafin kudi da tsaren tattalin arziki, shugaban algon na jiha, wakilan shiyya, da shugabannin kananan hukumomi, da dai sauran su.

Gwamnan ya bukaci membobin, musamman mahalarta daga waje da suka kware a harkokin siyasa da tattalin arziki, da su himmatu wajen yin aiki tare da dokar hukumar EPB gami da ba da shawarwarin samar da ci gaban hukumar ta ci gaba da aiki, ba kawai an yi la’akari da kasafin kudin bane, an kuma ba da fifiko kan bangaren fasaha da wasu shawarwari don cimma burin ci gaban Jiha.

Ya kuma nuna kwarin gwiwar cewa, hukumar tsara tattalin arzikin na bayar da gudunmawa sosai wajen ganin an cimma muradun ci gaban jihar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button