Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Rahotanni a Najeriya na cewa, an sake ganin bayyana riƙaƙƙen Ɗanbindigar nan Ɓaleri wanda ya addabi yankunan Zamfara, Sokoto, da Katsina, bayan Sojojin Jamhuriyar Nijar sun ce sun kama shi.
A makon da ya gabata ne dai, jami’an tsaro a Jamhuriyar Nijar suka ce sun yi nasarar cafke ƙasurgumin ɗanbindigar Ɓaleri, wanda ake nema ruwa a jallo a Najeriya.
Dakarun runduna ta musamman da ake yi wa laƙabi da Farautar Bushiya (Faraoutar Bushiya), sun ce sun kama shi ne a garin Rigar Kowa Gwani, da ke yankin Gidan Rumji a jihar Maraɗi.
To sai dai kuma DCL Hausa mai yaɗa labarai ta Internet ta ce “Ɓaleri ya sake bayyana, a cikin wani bidiyo da DCL Hausa ta samu, an nuna Bello Turji, yana daga hannun Baleri tare da musanta ikirarin kama shi”, in ji Jaridar.