Labarai
Trending

Cibiyar Binciken Kimiyyar Sinadarai Ta Ƙasa Za Ta Sake Baiwa Matasa Horo Kan Haɗa Kwallon Da Ake Wasanni Da Shi.

Daga Mu’azu Abubakar Albarkawa

Cibiyar binciken kimiyyar sinadarai ta ƙasa da ke Zariya wato National Research Institute Basawa Zaria, a karo na biyu ta sake shirya baiwa gwamman matasa maza da mata horo kan dabarun haɗa kwallon da ake amfani da shi wurin wasannin yau da kullum.

Taron horaswar,wanda na kwanaki 10 ne an kirkiro ne da nufin rage yawan matasa marasa aikin yi musamman a shiyya ta ɗayan Jihar Kaduna.

Kuma haka ɗaya ne daga cikin manufar shugaban cibiyar ta Narict Farfesa Joefree T Barminas.

A jawabin sa yayin kaddamar da fara shirin horaswar na kwanaki 10,Shugaba cibiya Farfesa Joefree T Barminas ya ce tsawon lokaci yana tuna irin alkaka mai kyau da ke tsakanin sa da makoftan makarantar wanda suka zama kamar yan uwa garesa,kuma hakan ne ya ce yake kirkiro da wasu abubuwa wanda a baya babu su don kyautata alakar da ke tsakanin su.

Farfesa Joefree ya ce sana’a shi ne jigon cigaban al’umma musamman da suke fatan dogaro da kan su,kuma matukar matasan suka riƙe wannan tsari za su ci gajiyar shi na tsawon lokacin rayuwar su.

A jawabin sa wurin taron kaddamar da fara shirin a harabar cibiyar da ke Basawa Zaria, mai kula da bangaren tuntuba kan aikace-aikace na cibiyar Olatunji Adenayi ya ce makasudin shirya taron shi ne don samarwa matasa ayyukan yi da za su dogara da kan su da sana’ar da zai amfane su tsawon rayuwa.

Ya ce tsarin nada alfanun da mahalarta da suka fito daga kananan hukumomi 8 na shiyya ta ɗayan Jihar Kaduna za su amfana da shi koda bayan sun kammala daukar horon na kwanaki 10.

Olatunji Adenayi ya bayyana fatan mahalarta taron su kasance masu kwarewa ta fannin abubuwan da aka koya masu a ƙarshen taron

Hakimin Gundumar Basawa kuma Barde Kerarriyar Zazzau Arc Haruna Bamalli wanda Sarkin Basawa Alhaji Isma’il Adamu ya wakilta ya yaba ne da ƙoƙarin da shugaban cibiyar NARICT ke yi don amfanin matasa maza da mata.

Ya kuma buƙaci wanda ake koyar da su sana’o’in su maida hankali game da abin da suka koya don amfanin kan su da ma sauran al’umma baki ɗaya.

Mujtaba Mukhtar Sambo da Isma’il Yakubu na daga cikin mahalarta taron,sun ce tsarin zai taimaka wurin samar da yawan matasa da suke dogaro da kan su.

Sun kuma yabawa shugaban cibiyar NARICT Farfesa Joefree T Barminas don samar da tsarin da kuma sauran ayyukan cigaba da yake yi koda yaushe a cibiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button