Notice: Constant DISALLOW_FILE_EDIT already defined in /home/martabaf/public_html/wp-config.php on line 98
"Haɗakar da ake ƙirƙira da nufin ƙalubalantar Tinubu a 2027 za ta rushe nan ba da daɗewa ba"-Ganduje - Martaba FM "Haɗakar da ake ƙirƙira da nufin ƙalubalantar Tinubu a 2027 za ta rushe nan ba da daɗewa ba"-Ganduje - Martaba FM

Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa Abdullahi Ganduje, ya yi zargin cewa jam’iyyar NNPP “ta mutu”.

Ya kuma yi ikirarin cewa jagoran jam’iyyar tsohon Gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso, zai shiga jam’iyya mai mulki.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Ganduje ya faɗi hakan ne a Abuja a ranar Talata, yayin da wata tawagar kungiyar Tinubu Support Group ta kai masa ziyara a sakatariyar APC ta ƙasa, inda ya ƙara da cewa jagorancin sa a shirye yake ya karɓi Kwankwaso a jam’iyyar.

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa ya jaddada cewa jam’iyyar mai mulki na ci gaba da karɓar fitattun ’yan siyasa, da ’yan majalisa daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

Ganduje ya kuma bayyana cewa haɗakar da ake ƙirƙira da nufin kalubalantar Tinubu a shekarar 2027 za ta rushe nan ba da daɗewa ba, inda manyan shugabannin ta za su dawo APC.

Ya ce, “NNPP ta mutu. Kuma za a binne ta nan ba da daɗewa ba. Ina fatan wajen da za a ajiye gawar, an riga an gina akwati.

“Abin da ya rage kawai shi ne a tona kabari. Kuma tuni suna tonon kabarin, nan ba da daɗewa ba za a kammala.

“Ko da hakan, jagoran NNPP shima ya ce bayan ya rasa kowa, yana son ya dawo mana, za mu karɓe shi, domin gida ne zai dawo.” inji Ganduje.

By Moddibo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *