Notice: Constant DISALLOW_FILE_EDIT already defined in /home/martabaf/public_html/wp-config.php on line 98
Jam'iyyar LP ta lashi takobin kayar da Tinubu a zaɓen 2027 - Martaba FM Jam'iyyar LP ta lashi takobin kayar da Tinubu a zaɓen 2027 - Martaba FM

Daga Sani Ibrahim Maitaya

Shugaban jam’iyyar Labour Party a jihar Ogun Chief Samuel Olaolu, ya bayyana cewa jam’iyyar adawar ta kuduri aniyar kifar da gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.

Olaolu ya gargadi Tinubu da kada ya dogara da masu cewa sake zaben sa a 2027 tabbatacce ne, yana mai cewa, “Gaskiyar magana ita ce ‘yan Najeriya sun gaji da rashin tsaro, yunwa da halin matsin tattalin arziki da ake ciki a kasar, kuma suna jiran 2027 ne kawai don su fitar da gwamnatin APC daga mulki.”

Ya bayyana hakan ne a ranar Assabar a taron manema labarai da aka gudanar a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Shugaban jam’iyyar Labour Party ya ce jam’iyyar ta shirya karɓar mulki daga hannun jam’iyyar APC mai mulki, yana mai cewa “’Yan Najeriya sun riga sun nuna kishin samun gwamnatin LP a 2027.”

A cewar sa, bayan hukuncin Kotun Koli da ta amince da kwamitin rikon kwarya karkashin jagorancin Sanata Nenadi Usman, jam’iyyar LP ce kawai ta rage a matsayin jam’iyyar adawa mai ƙarfi a Najeriya.

Olaolu ya ce, “Jam’iyyar Labour Party ta shirya karɓar mulki daga gwamnatin tarayya ta APC a 2027 domin ‘yan Najeriya sun riga sun nuna sha’awar samun gwamnatin LP. A yau a Najeriya, babu wata jam’iyyar adawa face Labour Party.”

“Kun san abin da ke faruwa a cikin jam’iyyar PDP yanzu, yadda masu mulki suka mamaye jam’iyyar. Haka ma suka so su mamaye mu, har sai da Allah ya ceci jam’iyyar ta bakin hukuncin Kotun Koli, wanda muke kallon sa a matsayin hukunci daga Allah.”

Ya kuma bayyana nasarar da LP ta samu a zaben shugaban kasa na baya, yana cewa, “A 2022, sun ce mu matalauta ne da ke tura sakwanni daga ɗakunan mu. Duk da haka, mun ga sakamakon da aka fitar a hukumance, mun samu fiye da kuri’u miliyan 6, kuma har yanzu muna da yakinin cewa mun ci zaben 2023.”

Game da halin da ƙasar ke ciki, ya ce “Saboda rashin tsaro, yunwa da matsin tattalin arziki, mafi yawan ‘yan Najeriya ba sa jin daɗin gwamnatin APC, kuma kowa ya san hanyar da ya kamata a bi.”

Ya jaddada cewa bayan hukuncin Kotun Koli da ya tabbatar da shugabancin kwamitin rikon kwarya na Nenadi Usman, jam’iyyar yanzu ta mayar da hankali wajen sake gina tsarin ta, da kuma haɗa kai domin yi wa ‘yan Najeriya aiki yadda ya kamata.

Olaolu ya ce, “Kwamitin rikon kwarya na Nenadi Usman ya kuduri aniyar tabbatar da sauyin mulki cikin sauƙi, inganta haɗin kai, da samar da yanayi da kowanne mamba zai sami damar bayyana ra’ayin sa.”

By Moddibo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *