Labarai
Trending

Gwamnatin Yobe ta soke lasisin makarantu masu zaman kansu a faɗin jihar

Gwamnatin Yobe ta soke lasisin wasu makarantu masu zaman kan su da ke jihar, tare da kiran masu makarantun su bi tsarin doka da odar da gwamnati ta shinfiɗa don neman sabon lasisi.

Gwamnatin ta kara da cewa daga yanzu duk wasu lamura na makarantar za su dinga tafiya kafaɗa-da-kafaɗa da makarantun gwamnati, ba za a ƙara ba su damar gaban kansu ta fuskar dokoki da sauransu ba.

Kwamishinan ilimi na jihar Dakta Muhammad Sani Idriss, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, a ganawar da suka yi da masu makarantu masu zaman kansun, a makarantar sakandaren gwamnatin tarayya ta GGC Damaturu.

Ya ƙara da cewa babu wata makarantun da za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta ba tare da sabon lasisi da bin dokar da gwamnatin jihar Yobe ta gindaya ba.

Ya ce, “ mun soke lasisin makarantu masu zaman kansu, dan haka za su sake sabo.

A baya an ba su wannan damar kai tsaye, amma an bukaci su bi wasu dokoki amma hakan bai samu ba, shi ya sa muka ɗauki wannan matakin.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button