Gwamnatin Najeriya ta bayyana rashin jin dadin ta game da matakin da kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC suka dauka na fara yajin aikin a fadin kasar, duk da umarnin da kotun ma’aikata ta bayar na kada su yi yajin aiki.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin ta bayyana matakin a matsayin wata alama ta girman kai da ƙoƙarin shafa wa gwamnati kashin kaji., kamar yadda BBC ta rawaito.
Sanarwar wadda ta samu sa hannun mai taimaka wa shugaba Tinubu kan yaɗa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga ta ce “yajin aikin fatali ne da umarnin kotu da tozarta ɓangaren shari’a.”
Ta ƙara da cewa “Bai kamata ƙungiyoyin biyu su hukunta ƙasar baki daya ba kan wani lamari na ƙashin kai da ya shafi shugaban ƙwadagon, Joe Ajaero, wanda aka kai wa hari a Owerri”
Gwamnati ta jaddada kudirinta na gudanar da bincike kan harin da aka kai wa shugaban ƙungiyar Ajaero, inda ta ce babban sufeton ‘yan sanda ya bayar da umarnin a gudanar da bincike, kuma an canja kwamishinan ‘yan sandan jihar Imo.
Gwamnatin ta kuma jaddada cewa, yajin aikin, wanda ya bijirewa umarnin kotu, na nuni da rashin mutunta bangaren shari’a, kuma ya saɓawa ka’idojin kungiyar kwadago a tarihi.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.
-
Gwamnan Kano ya amince da murabus ɗin Kwamishinan Ma’aikatar Bibiya da tabbatar da Nagartar Aiki.
-
Gwamna Zulum zai saka tallafin man fetur ga manoman yankin da rikicin Boka Haram ya shafa.
-
Sarakunan da Fintiri ya naɗa bayan ƙirƙirar masarautu 7 a jihar Adamawa.