Labarai

Sanata Shehu Buba Ya Tallafawa Ɗalibai 364 Da Kuɗin Zana Jarrabawar JAMB.

Ɗaliban sun fito ne daga ƙananan hukumomi 7 na Bauchi ta kudu

Daga Muhammad Sani Abdulhamid, Bauchi

Dalibai 364 ne suka samu tallafin kudin zana jarabawar JAMB daga Sanatan Bauchi ta Kudu, Sanata Shehu Buba Umar, wanda ɗaliban suka fito daga kananan hukumomi bakwai na shirya Bauchi ta kudin.

Umar Auwal, shine shugaban shirin Shehu Buba Education Endowment support wanda su ka yi aikin zakulo daliban da suka ci gajiyar shirin.

A cewar sa, wadan da aka biya wa kudin zana jarabawar ƴa’ƴan talakawa ne wanda suna da hazaka kuma sun gama makarantar sakandare amma ba su da halin zana jarabawar ta JAMB don cigaba da karatu.

Umar yace Sanata Shehu Bub, na da niyar cigaba da biya wa duk wanda yayi kokari a jarabawar kudin makaranta don cigaba da karatu, sai ya jinjina masa bisa na miji kokarin da yake yi a jihar Bauchi.

Wasu iyaye da ɗaliban da suka ci gajiyar tallafi sun nuna jin dadin su matuƙa bisa abinda Shehu Buba ya su da addu’ar Allah ya saka masa da mafificin alheri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button